Solomon Dalung Yayi Dana Sani

Barista Solomon Dalung

Ministan matasa da wasani na Najeriya Solomon Dalung, ya ce yayi dana sani da ya rushe hukumar wasani ta Najeriya, watau NSC.

Ya furta haka ne a wata hira da aka yi dashi a gidan Talibijin na Najeriya, NTA, yana mai cewa hukumar na da rawar takawa a sabon tasawiran wasani a Najeriya.

Dalung, ya kara da cewa hade ma’aikatar Wasani da na matasa a lokacin da ya zama Minista ne ya haifar da kwamitoin da zai tsara hade ma’aikatun guda biyu sannan abinda ya fito daga kwamitin rahoto ne kawai ya zuwa yanzu.

Ya ce yin garambawul daga tushe ne sahihiran hanyar samun ci gabar ma’aikatar.