Shararen dan wasan kasar Portugal mai taka leda a kungiyar Real Madrid, Cristiano Ronaldo, ya bayyana cewa yana daf da dawowa ci gaba da taka leda bayan jinyar da yani na tsawon watani biyu sakamakon raunin da ya samu a guiwar sa yayin gasar cin kofin nahiyar kasashen Turai, wanda aka gudanar a kasar Faransa, a watan Yuli da ta gabata.
Cristiano Ronaldo, ya bayyana haka ne ta shafin sada zumunta na Istagram.
Koda yake bai sami damar fafatawa a wasan da kungiyarsa ta Real Madrid ta yiba na la liga, tsakanin ta da Real Sociedad da Celta Vigo ba sai dai ana sa ran cewa nan da dan wani lokaci Cristiano Ronaldo, zai jawo ci gaba.
Ita kuwa kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, ta nuna danuwarta bisa raunin da dan wasanta Lionel Messi, ya samu a wasan da kasar sa ta buga da kasar Uruguay, a neman shiga cin kofin kwallon kafa na duniya inda suka samu nasarar doke Uruguay, din da ci daya mai banhaushe.
A can baya dama kungiyar ta Barcelona, ta fitar da sanarwar cewa dan wasan bazai samu damar fafatawa saboda raunin da yake fama dashi ba amma daga bisani Argentina tayi amfani dashi don ci gaba da wasan yadda yanzu bazai samu damar fafatawar da zasu yi da kasar Venezuela, ranar laraba mai zuwa.
Your browser doesn’t support HTML5