An bukaci matasa ‘yan makarantar gaban da sakandare da su jajirce wajan kara neman sana’oin dogaro da kai akan ilimin da suke nema domin su inganta kawunan su da kuma al’ummominsu.
Shukiriya Labaran wata daliba kuma matashiya mai sana’ar kunun gyada, kunun aya Zobo, domin dogaro da kai ta ja hankalin ‘yan uwanta matasa mussamam ma mata domin saukakawa juna tsakanin miji da mata.
Ta ce burinta ta inganta sana’arta na sanya wa sana’ar ta ta suna tare da tabbatar da cewar hukuma lura da ingancin abinci sun san da sana’ar ta, domin amfanin karatun da take yi domin ta canza yadda aka sana’oin zuwa na zamani.
Ta kara da cewa tabbas ilimi na da tasiri a sana’a tana mai cewa idan matasa suka rungumi koyan sana’a, idan suka kammala karatun su aiki ba zai zama da damuwa ba.
Your browser doesn’t support HTML5