Meke Sa Kyawawan 'Yan-Mata Rasa Samari Ko Gidan Aure?

Abun da ban mamaki da daure kai, me kesa ‘yan mata kyawawa, basu iya rike samari ko zaman gidan aure? Sau da yawa sai aga ‘yan mata da suke da kyau, basu zama da saurayi daya, yau agan su da wannan gobe a gansu da wani. Ba kuwa dan komai ba, sai dan wasu dalilai na son kai, sukan samu kansu a cikin hakan ne a dalilin wata rayuwa da suka daukar ma kansu.

Abu na farko da kansa ‘yan mata rasa samari, kyawawan ‘yan mata sun cika laulayi da rashin son wahala, gasu da son duk wani abu da zasu nuna ma saurayi sun san abubuwa masu tsada.

Suna da tsadar rayuwa wajen zama, don kuwa basu cika son abu da bashi da tsada ba, koda saurayi ko miji zai saya musu abu basu son mai arha, suna da son nunama abokan su isa, hakan kan sa maza rabuwa da su a wasu lokutta.

Kyawawan ‘yan mata na da son kai, basu cika son hada kansu da wasu ba, idan akazo wajen rabon abu sun fison a basu nasu fiye da na kowa. A gidan aure kuwa su kance basu son haihuwa, don kada kyau din su ya ragu ko su rasa tsarin jikin su. Gasu da zabin wane irin saurayi zasu zauna da, don suna ganin kamar sai anyi da su.