Ilimi Shine Gadon Bayan Kowace Irin Sana’a

Isa Ayagi

Ilimi shine gadon bayan kowace irin sana’a, Isa Ayagi, matashi kuma dalibi wanda ya koma makaranta domin karo ilimi ya bayyana cewa cigaba a kowace irin sana’a, yana samuwane idan da ilimi.

Mawakin ya bayyana haka ne a tattaunawar su da Baraka Bashir, wakiliyar Dandalinvoa, inda yake cewa ya lura mafiya yawan lokuta idan ana zancen ilimi da wasu mawakan sai a tarar ba suyi nisa ba a harkar ilimin zamani, hakan ne ya tunzura shi komawa makaranta don ya karo ilimi.

Ya ce yana yin waka ne domin ya fadakar ya kuma ilimantar da jama’a akan harkokin yau da kulum, ya kara da cewa ilimin zamani zai taimaka gaya sauya tunani al’umma ga ci gaba.

A fanninmu na tsegumi kuwa a jiya ne fitattacen dan wasan barkwancin nan Bright Okocha, wanda aka fi sani da basket mouth barayi sun masa ta’adi a gidansa da ke Lekki a jihar Lagos.

Your browser doesn’t support HTML5

Ilimi Shine Gadon Bayan Kowace Irin Sana’a - 4'39"