A ci gaba da wasan neman cin kofin duniya na shekara 2018, da ake yi kungiyar kwallon kafa ta Brazil, ta doke Columbia, da ci biyu da daya inda da wasan ta mai suna Mirinda, ya fara jefa kwallo a ragar Columbia cikin minti biyu da fara wasa.
A cikin minti na saba’in da biyar a cikin wasan Neymar, dan wasan Brazil, ya jefa kwallon da ya baiwa Brazil nasarar cin Columbia biyu da daya.
Kungiyar Uruguay, ta lallasa Paraguay, da ci hudu da babu, Venezuela kuwa sun tashi kunnen doki biyu da biyu Argentina, kamar yadda Netherland, suka yi daya da daya da Sweden.
Switzerland, kuwa ta sami nasara akan Portugal, ne da kwallaye biyu da babu, yayin da Belarus suka tashi babu ci tsakanin su da Faransa, kungiyar kwallon kafa ta Cyprus, kuwa ta sha kashi, a hannun Belguim da ci ukku da nema
Your browser doesn’t support HTML5