WASHINGTON, DC —
Sabon mai harar da ‘yan wasan Najeriya, Gernot Rohr, dan kasar Jamus, ya ce Najeriya, nada bukatar hado kan duk kwararrun ‘yan wasanta da suke kasashen duniya, domin su taimakawa kasar.
Najeriya, dai tana cikin rukunin da ake mata taken rukunin mutuwa, inda suke hade da Algeria, Kamaru da Zambia, inda zasu fafata neman shiga gasar cin kofin duniya na 2018, wanda za’a yi a kasar Rasha.
Ranar 3, ga watan gobe watau Oktoba, Najeriya, za tayi tataki zuwa kasar Zambia, domin domin karawa da kasar a daya daga cikin wasaninta na naman gurbin a gasar cin kofin duniya.
Your browser doesn’t support HTML5