WASHINGTON, DC —
Dan wasan kwallon tebur na Najeriya, Haruna Quadri, yanzu shine na ashirin da biyar a duniya, daga na arba’in, kamar yadda hukumar kwallo teburi ta duniya ta wallafa.
Quadri, wanda ya sami maki 2305, a watan Agusta, yanzu yana da maki 2457, wanda ya bashi damar zama dan Afirka na farko, da zai kasance ciki mutane ashirin da biyar a duniya a faggen wasan kwallon teburi.
A wasanin Olympic, na bana Quadri har wasan kusa da na karshe inda Ma Long, wanda yake shine na daya a duniya, wani dan Najeriya, wanda shima ya yiwa Najeriya wasa a gasar Olympic yanzu shine na 106, daga na 120.