Tsohon da wasan Brazil, kuma tsohon mai bugawa kungiyoyin Barcelona da Inter Milan Ronaldinho, dan shekara talatin da shida na shirye shiryen yin retaya daga taka leda.
Ronaldinho, ya ce lokaci yayi da yakamata sun sagale takalman taka leda su barwa matasa domin girma ya kama.
Kafin wannan lokaci dai Ronaldinho, ya sami nasarori da dama a yayin da yake bugawa kasar sa wasa da kuma kungiyoyin da ya yiwa wasa, inda ya sami nasara cin kofin “Copa America” a shekara 1999, wa kasar sa ta Brazil, wasan da akayi a kasar Mexico.
Sai kuma shekara ta 2002, inda ya samu nasara cin kofin duniya, wanda akayi Koriya da Japan, sai shekara ta 2005, a FIFA Confederation inda ya sami nasarar lashewa kasar sa a Jamus.
Your browser doesn’t support HTML5