Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, ta kasance kungiyar kwallon kafa ta farko a kasar Ingila da ta sami fiye da fam miliyan dari biyar a shekara daya.
Koda yake kungiyar ta gaza samun gurbi a gasar zakarun a karo na biyu a cikin shekaru ukku, amma ta kashe makudan kudade wajan tabbatar da ganin cewa kungiyar ta sami ‘yan wasa na kwarai.
Cikin manyan kamun da kungiyar tayi sun hada da Paul Pogba, Zlatan Ibrahimovic,Eric Bailly da Henrikh Mkhitaryan.
Maitaimakin shugaban kungiyar Ed Woodward, ya ce karfin arzikin kungiyar ya nuna cewa kungiyar zata iya kai labari ko babu kudaden daga lig din zakaru.
Manchester United, da kamfanin Adidas sun rattaba hannu akan wani kwantrigin shekaru goma (10) a shekarar 2014, wanda ba’a taba samun irin sa ba.