Wani bala’i, ya faru a unguwar Oke Fia, a garin Osogbo, da cikin jihar Osun, inda wani dan Okada, ya farkewa wani mai babur ciki, bayan da suka yi taho mu gama.
Shi dai wanda aka farkewa ciki da wukar, mai suna Remi Gbadamosi, yanzu haka yana asibiti, yana neman ransa.
Jaridar Punch, ta ruwaito cewa wata ganau Fatima Jamiu, ta ce bayan da hadarin ya faru sai suka fara fada na tsawon kimanin mintuna biyu, daga bisani said an Okadan, ya fito da wuka ya farkewa abokin fadan nasa ciki.
Ganin aika aikan da yayi sai ya nemi ya guda sai jama’a da ‘yan Sandan dake kusa suka damke shi akayi gaba dashi ofishin ‘yan Sanda.
Da yake tabatar da labarin Kwamishinan ‘yan Sandan jihar Femi Oyeleye, za’a gurfanar da wanda ya aikata wannan aika aikan bayan an kammala bincike.