Ya Jefa Dan Shekaru Ukku Cikin Kogi

Wata kotun majistare dake Abakaliki,ta sa a tsare wani mai suna Ogobuchi Ogbonna, dan shekaru ashirin da biyar(25), a gidan yari a bisa zargin cewa yayi sanadiyar mutuwar wani dan, dan uwansa mai suna Wisdom Wilson, a wani kogi.

An ce Ogbuchi ya daura wa Wisdom, dan shekaru ukku diutse a kukunsa ya jefa shi cikin kogin dake yankinsu wanda yayi sanadioyar mutuwan yaron.

Lamarin dai ya faru ne a Ndievor-Nchoko Igbeagu, a karamar hukumar Izzi, a yankin Abakaliki, dake jihar Ebonyi.

An gurfanar da Ogobuchi, a gaban kotu, ana tuhumarsa da laifin yin sanadiyar mutuwar Wilson, wanda laifin na dauke da hukumci a karkashin sashe na 33, sakin layi na daya a dokar jihar Ebonyi.

Mai shara’a Mr Nnachi Olughu, ya bada umarin a tsare shi a gidan yari, a kuma maida takardan karar ga Darakatan gabatar da kara na Gwamnati domin daukar mataki nag aba domin a cewar mai shara’an, kotun bata da hurimin sauraran karar.