A yau litini jami’an tsaro sun sami nasarar cafke matashin nan mai shekaru 28, da haihuwa wanda ake zargi da kai harin bam a jihar New York da New Jersey, a kasar Amurka a wani samame da ‘yan sandan kasar suka kai har ya samu raunika a sakamakon musayar wuta.
Matashin dan kasar Somali da ake zargi da kai hareharen wanda suka afku a ranar Asabar sun hada da sukar jama’a da dama da wuka da kuma fashewar wani abu da ake zargi keda nasaba da bam, kuma ake danganatawa da ‘yan ta’addan ISIS.
A yayin da yake halartar taron majalisar dinkin duniya da ake kan gudanarwa a birnin New York, shugaba Barack Obama ya aika da sako ga daukacin Amurkawa cewar kada su yi fargaba a dukkan hare haren da aka kai.
An nuna hotunan matashin mai suna Ahmed Khan Rahami mai shekaru 28, da haihuwa, kwance da bandeji a kafadar sa ta dama a kan gadon daukar marasa lafiya a cikin motar data dauke shi zuwa asibiti.
Rahotanni sun bayyana cewa jami’an ‘yan sanda biyu sun sami raunika a yayin da sukai musayar wuta kafin a sami nasarar kamam shi.