A wannan yanayin da lokacin da ake ciki, na iya zama wani lokacin matsatsi ga shugaban kungiyar kwallon kafar “Manchester united” Mr. Jose Mourinho, A karon farko ya bama ‘yan wasan kungiyar shi mamaki, na rashin fita fagen daga dasu, biyo bayan rashin nasarar su a wasan da suka buga da kungiyar Chelsea.
‘Yan wasan dai suna cike da bakin ciki, a yayin da wasan su aka tashi da ci hudu da babu 4-0, hakan yasa sun yi mamamkin rashin fitowar shugaban nasu, don basu karfin gwiwa a yayin atisaye. Wannan wani abu ne da ya bama Koci din mamaki, domin kuwa a duk iya tsawon shekarun shi na zama koci, bai taba ganin abu makamancin haka ba.
Wasan dai da aka gwabza, a filin wasan “Stamford Bridge” abun dai har ya kai ga sai da shugaban ya kira ‘yan wasan nashi “Yara” ganin irin abun kunyar da su kayi a wannan kakar ta “Prenier League” mataimakin koci din Mr. Rui Faria, shi ya jagoranci tawagar ‘yan wasan, inda shi kuma shugaban yake zaune a ofis yana kallon atisayen ‘yan wasan.
An bayyanar da shuagabn dai bashi da burin sake zubin kungiyar, tun bayan karbar kungiyar da yayi a hannun tsohon shuagabn ta Mr. Louis Van Gaal, a nan kusa.