Rahoton da shafin hukumar binciken manya-manyan laifufuka ta kasar Birtaniya, suka ruwaito. Yana nuni da cewar tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafar Super Eagle Mr. Efetobore Sodje, yana hannun jami’an hukumar a tsare.
Tarihin wasan kwallon kafa a Najeriya, ba zai taba mantawa da dan wasa Sodje ba, saboda wasannin da ya buga a wasan zakaru na cin kofin kasashen Afrika a shekarar 2000, da wasan cin kofin duniya a kasashen Korea ta kudu da Japan 2002. Kuma shine dan wasa daya tilo, da yake saka bandana a cikin fagen wasa.
Shi dai tsohon dan wasan yana tsare ne tare da kannan shi su uku 3, Bright mai shekaru hamsin 50, da Stephen da ke da shekaru arba’in da biyu 42, kana da Samuel mai shekaru talatin da bakwai 37. Yanzu haka ana tuhumar su da laifin zanba cikin aminci.
Hukumar ta gabatar da bincike na tsawon shekaru uku 3, inda ta same su da laifin zamiyar makudan kudade da sunan kungiyar “Sodje Sport Foundation” wadda aka kirkira dan taimakama matasan Najeriya, masu sha’awar kwallon kafa a fadin duniya.
Tun a watan Yuli, ne aka kamasu, yanzu haka ana sa ran zasu gurfana a gaban kuliya. Shi dai dan wasan ya samarma kamfanin nashi, takardun zama kamfani mai zaman kansh a shekarar 2010. Amma zuwa shekarar da ta gabata an kwace lasisin kungiyar, biyo bayan wasu haramtatun abubuwa da aka aiwatar a kungiyar.