Sabuwar Allurar Kayyade Iyali Domin Maza

Sakamakon wani sabon bincike a Geneva, kasar Switzerland ya bayyana cewa sabuwar allurar kayyade iyali, ko hana haihuwa da ake yiwa maza na aiki tamkar yadda magani yake aiki jinsin mata, sai dai matsalar ita ce maganin yana haifar da damuwa ga wanda aka yi wa allurer.

Allurar na aiki a jikin maza ne ta hanyar rage yawan kwayoyin halitta da namiji kan fitar a lokacin jima’i saduwa, wanda hakan zai hana daukar ciki.

Yayinda aka gudanar da bincike tsakanin ma’aurata 266, guda 4 ne kadai daga ciki suka sami haihuwa, da alamun maganin zai yi tasiri kwarai sai dai za’a dauki lokaci kafin ya sami karbuwa.

Likitoci sun bayyana cewa wannan allura zata taimaka wajan rage banbanci tsakanin namiji da mace da kuma daidaita al’amurran zamantakewa ta wajan harkokin kula da iyali.

Sai dai a cewar likita mai bincike Dr Tara Narula, ba karamin aiki bane domin jikin namiji baligi na samar da kwayoyin halittar har guda 1,500 cikin dakika guda kuma guda daya ake bukata domin daukar ciki, dan haka a cewar sa, sai an yi taka tsantsan.