Fiye Da Rabin Mutane A Duniya Na Amfani Da Wayar Hannu, Amma Basu Da!

Wayoyin Hannu Da Yanar Gizo

A cewar wani rahoto da shashin sadarwa na kasa-da-kasa, da majalisar dinkin duniya suka fitar, kimanin sama da kashi tamanin da hudu 84% na mutane a fadin duniya, suke da wayar hannu. Amma kasa da kashi arba’in da bakwai 47% ne kawai ke da yanar gizo a wayoyin su, bisa dalilin tsadar data, ko wasu dalilai masu nasaba da hakan.

Rahoton ya kara da cewar, tun a shekarar 2015, ne wayoyin hannun suka rage tsada, wanda aka samu faduwar kudin waya da ya kai kimanin kashi ashirin 20% a kasashe masu tasowa a duniya. Haka sinadaran yanar gizo sun kara sauki, sai dai hakan na da tsada a kasashe masu tasowan.

Alkalumma sun bayyana cewar, kimanin kasashe dari da saba’in da biyar 175, ne aka samu cigaba a harkar sadarwa ta zamani, majalisar dinkin duniya, ta bayyanar da matukar muhimanci wayar hannu da yanar gizo, ga cigaban duniya da al’uma, haka suna taimakawa wajen tattalin arzikin kasa, ilimi da kara samun wayewa a fadin duniya.

Don bama mutane damar amfani da yanar gizo, a duniya sai an kawo hanyoyin dai daito na tattalin arziki, a cewar shugaban sashen sadarwa na kasa-da-kasa a majalisar dinkin duniya, Mr. Houlin Zhao, ilimi da tattalin arziki sune alkalumman da za’ayi amfani da su, wajen tantance ko mutane na amfani da yanar gizo.

Yanar gizo da kimiyya da fasaha, zasu taimaka matuka wajen cinma burin majalisar dinkin duniya goma sha bakwai 17, da suka sa a gaba. Majalisar dai nada burin kawo karshen talauci, da daidaito a tsakanin al’umar duniya, kamin shekarar 2030.