Kamfanin Netflix Zai Fara Ba Mutane Damar Sauke Fina Finai A Wayar Hannu

Kamfanin hayar fina finai akan yanar gizo ta Netflix zai fara barin mutane su sauke fina finai akan na’urorinsu ta yadda zasu kalla ba tare da sunyi amfani da data dinsu ba, biyo bayan dadewar da mutane sukayi suna neman kamfanin ya aiwatar da hakan.

A jiya Laraba ne Netflix yace shahararrun fina finai irin su “Orange Is the New Black,” da “The Crown” zasu zamanto cikin jerin fina finan da masu shiga dandalin domin biyan kudi suyi kallo zasu iya saukewa a na’urorinsu. Abin da mutane zasu yi yanzu shine su shiga su sabunta manhajar Netflix a cikin na’urorinsu kafin su fara iya sauke fina finai.

Yanzu haka dai akwai jerin irin fina finan da mutane zasu iya saukewa kadai, amma kamfanin yace nan gaba za a kara wasu fina finan. Baki daya masu biyan kudi a dandalin Netflix domin suyi kallo dake fadin duniya zasu iya amfani da wannan garabasa, domin kallon abin da suke so ba tare da suna kan yanar gizo ba.

Masu amfani da wannan dandali dai sun dade suna neman kafanin ya basu wannan dama, har shugaban kamfanin yace wannan abune da bazai yiwu ba. daga baya kuma cikin watan Afrilu yace kamfanin zai yi tunani akai. Kasancewar habakar kamfanin a kasashen duniya yasa ya amince saboda sauwakawa mutanen da basu wadatar yanar gizo.

Your browser doesn’t support HTML5

Kamfanin Netflix Zai Fara Ba Mutane Damar Sauke Fina Finai A Wayar Hannu