Shugabar Kamfanin Yahoo Marissa Mayer Tana Fuskantar Tirjiya!

Shugabar Kamfanin Yahoo Marissa Mayer.

Shahararren kamfanin sakon yanar gizo, Yahoo sun dauki alwashin kin biyan shugabar kamfanin kudaden tukwicin aikin ta na tsawon shekaru, biyo bayan sakaci da ta nuna a aikin ta, da aka samu wata baraka na satar bayanai a shekarar data gabata.

Shugabar kamfanin Marissa Mayer, ba zata karbi wadannan makudan kudaden ba, na shekarar da ta gabata, wanda suka kai kimanin dallar Amurka milliyan biyu $2M kimanin dai-dai da naira billiyan tara. Hakan dai nada nasaba da irin matsalar da kamfanin ya shiga, karkashin jagorancin ta a shekarar 2014.

Haka shima shugaban tsare-tsaren na kamfanin ya ajiye aikin shi, babu wasu kudaden sallama da za’a bashi, ana tsanmmanin cewar yayi sakaci matuka, a yayin da ‘yan kutse suka samu nasarar satar bayanan mutane.

Wata babbar matsala itace yadda kamfanin basu sanar da mutane, da yawaba dangane da matsalar kutsen ba, mutane ashirin da shida kawai suka sanar. Wanda an samu mutane sama da milliyan dari biyar, a fadin duniya da suka fuskanci wannan matsalar. Baki daya cikin shekaru biyu sama da mutane billiyan daya suka fuskanci matsalar satar bayanai, dake da asusun bayanai na Yahoo.