Daliban Jami'ar Lagos Sun Gudanar Da Zanga Zangar Lumana

Daliban jami'a masu zanga zanga

Daruruwan daliban jami’ar Lagos sun gudanar da zanga zangar lumana a kofar shiga jami’ar domin neman a dawo da wasu daliban goma sha daya (11) da aka dakatar daga makarantar a bara. Kawo yanzu dai jama’ar ta dakatar da harkokin kungiyar daliban jami’ar.

A lokacin wannan zanga zangar dai ‘yan Sandan Najeriya sun ja daga da daliban a kofar shiga jami’ar, inda suka hana dalibai da sauran masu harkokin yau da kullum shiga harabar jami’ar.

Kamar yadda wakilin muryar Amurka Babangida Jibrin, ya ruwaito yayi kokarin shiga harabar jami’ar amma jami’an ‘yan Sanda sun hana.

Wani tsohon dalibin Jami’ar, Barrister Idowu, ya bayyana rashin jindadinsa dangane da matakin da hukumomin jami’ar suka dauka na dakatar da daliban. Ya kara da cewa hukumomin jami’ar sun san da komai domin sune suka turo jami’an ‘yan Sanda suka hana dalibai shiga jami’ar domin sun san cewa ana adawa da matakin nasu.

Koda yake ‘yan Sandan basu dauki wani mataki na nuna karfi bag a daliban amma dai sun hana daliban shiga duk kokarin jin ta bakin mahukuntan jami’ar ya cutura.

Your browser doesn’t support HTML5

Daliban Jami'ar Lagos Sun Gudanar Da Zanga Zangar Lumana - 2'12"