Ana Amfani Da Sabbin Hanyoyin Kimiyya Don Yaki Da Mallakar Filaye!

Sabbin Kirkirar kimiyya daga Jirgi mara matuki mai dauke da na’urar daukan hoto, zuwa karbar bayanai ta motocin haya, na zama wani makami a duniya, na yaki da kuma habaka hakkin mallakar filaye, da yaki da talauci, cewar kwararru a ranar Litinin.

Cigaban da ake samu wajen hangen duniya, gamayyar na’ura mai kwakwalwa, da kuma bayanai masu karfi da ake samu ta Nau’ra mai kwakwalwa, wanda ya hada da cikakken zanen taswira domin amfani wajen tafiye tafiye, wanda ba’a taba tunanin samuwar su ba a baya. Masana akan harkokin Taswira suka bayyana a taron Bankin duniya akan kasa da kuma talauci.

Bayanan da ake karba zasu iya zama ababan amfani, wajen taimakawa a gabatar da bayanan muhallai, da kuma filaye tare da sunaye cikin tsari a kasashen da basu da tsarin mallakar filaye, a gwamnatance ko kuma takardun shaidar izinin amfani da filayen.

Jirgi mara matuki mai dauke da naurar daukan hoto, wanda ake amfani da shi wajen ganin yadda yanayin kasa yake, karami ne mai kama da abin wasan yara, amma yana da matukar amfani, anyi amfani da shi wajen auna yadda ake amfani da filaye, da kuma tsara su a Afirka cewar Edward Anderson, kwararre kuma babban jami’in bankin duniya bangaren Bala’i.