Kamfanin Samsung Zasu Siyar Da Wayar Galaxy 7s, Kan Farashin Tsohuwar Waya

Shahararren kamfanin wayoyi da wasu kanyan kimiyya da fasaha a fadin duniya Samsung, sun bayyanar da muradin su na sayar da wayar Galaxy Note 7s, wadda aka fi sani da ‘Landon Used’ sakon han. Biyo bayan kiranye da akayi, na miliyoyin wayar da kamfanin yayi a ‘yan kwanakin baya, sanadiyar matsalar batiri da wayar take da.

Kimanin watanni biyu, bayan kaddamar da sabuwar wayar ta Galaxy Note 7s, kamfanin su kayi kiranye na wayar a fadin duniya, wanda a lokacin kudin wayar ya fara daga dallar Amurka $900 kimanin naira dubu dari hudu.

Bincike da suka gudanar da ya nuna cewar, an samu wasu matsaloli a yadda aka hada batirin wayar, a tsakanin kamfanoni biyu da suke hadama kamfanin batirin waya, wanda hakan ya sa wayoyin basu da karfin rike caji yadda ya kamata.

Masu bincike na kamfanin, da na waje sun tabbatar da cewar wayar bata da matsala a cikin injin nata, babbar matsalar ta a batiri ne kawai. Hakan yasa kamfanin zasu maida wayar kasuwa, don siyar da wayoyin a farashin tsofaffin wayoyi, amma a zahiri sababbin wayoyi ne.