China Za Ta Samar Da Fasahar Sarrafa Takardar Tsarki A Bandaki

Hukumar kula da yawon bude ido ta kasar China, ta yi gargadi da nuna gajiyawa da yadda ake satar takadun da aka ajiye na katse bayan gida a ban daki wato ‘Toilet Paper’ a turance. Hakan yasa hukumar samar da wata sabuwar na’ura na kallon jikin mutun don tantance adadin yawan takardar da zai bukata.

Ita dai na’urar za kuma ta taimaka wajen tantance tsaftar ban dakunan da ake da su a kowane wuri haduwar jama’a, na’urar za ta tantance irin warin da ake samu a cikin bayi yayin da mutane ke amfani da bayin.

A cewar Zhan Dongmei, na cibiyar da ke horar da masu kula da yawon ido a kasar ta China, yace mutane na daukar ban dakin mutane a matsayin wajen da ba’a kula da shi, don haka mutane sai su yi ta yin kazanta a ciki.

Hakan na haifar da cututtuka da dama a cikin al’umah, don haka lokaci ya yi da za’a fara tsaftace ban dakunan don samun yanayi mai inganci a cikin al’umma. Sau da yawa mutane kan dibi takardun katse bayan gidan don wasu bukatu nasu na daban.

Wannan wani sabon tsari ne da zai dinga ba mutane takardar da ta kai tsawon tafin kafar mutun duk bayan mintoci tara, wanda sai mutun ya kalli kyamarar da ke jikin na’urar kamin ta bashi takardar.

Mutane da dama kan dauki takardun da yawa don amfani da su a duk lokacin da bukatar hakan ta zo musu, da tunanin cewar suna iya zuwa don yin amfani da takardar su tarar ta kare. Mr. Zhan ya kara da cewa, idan har za’a samar da takardar a wadace kuma da sabon tsari to za su magance matsalar.