Kamfanin 'Snapchat' Ya Inganta Manhajarsa

Kamfanin shafin zumunta na ‘Snapchat’ sun kaddamar da wani sabon tsari a manhajar su, wanda mutane zasu iya lalubo hotuna, da bidiyo da mutane suka saka a shafufukan su don jama’a.

Hakan ya biyo bayan wani sabon tsari da shafin zumunta na facebook, suka kaddamar da mutane zasu iya amfani da shafin su, wajen daukar hoto da kuma damar gyara hoton duk a shafin yanar gizo.

Kamfanin sun bayyanar da hakan ne a wani bayani da suka fitar a shafin su, wanda ke cewar mutane yanzu zasu iya amfani da manhajar ta su don zakulo hoto da bidiyo, da wasu suka sa, kana zasu iya samun duk wadannan idan suka shiga babin ‘Our Story’ labarin mu.

Mutane zasu iya amfani da wannan sabon tsarin na ‘Our Story’ don duba wasu abubuwa da mutane suka saka a baya, abu da kawai mutun yake bukata shine, yayi matashiya da irin labarin da yake bukata. Kamar mutun ya sa labarin wasan kwallo ko sunan kungiyar da yake sha’awar labarin su.