Ahmad Gwamnati: Matasa Kada Ku Raina Sana'a Koya Take.

Ahmad Dahir Sharada

Ahmad Dahir Sharada, wanda aka fi sani da Ahmad Dahiru Gwamnati, ya ce ya taso ne da basirar waka, ba koya mishi akayi ba, sha’awa ce ta ja shi ga harkar, har ya zamanto ya lakanci waka.

Mawakin ya bayyana haka ne, a yayin da yake zantawa da wakiliyar DandalinVOA, da safiyar yau a Kano.

Ya ce waka baiwa ce a wajensa, a ta bakinshi mafi akasarin wakokinsa, yana yin su ne akan lafiya, inda yake cewa idan ya fara waka da kalamun ya-ya da hakan yake karewa.

Ahmad ya ce akasarin wakokinsa yana yinsu ne domin isar da sakonnin rayuwa, ga ‘yan uwansa matasa, mussamam ma a bangarorin da suka shafi harkar sana’a, da sauran rayuwa.

Ya kara da cewa, yana isar da sakanonnin zamantakewa da kuma rashin raina sana’a a tsakanin matasa.