Shugaba Buhari Ya Karrama Mata 'Yan Wasa

Shugaba Buhari da 'yan wasan kwallon kwando D' Tigress

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, wanda ya karbi tawagar “D’Tigress” mata ‘yan wasan kwallon Kwando na Najeriya, a fadar Gwamnati na Aso Rock, dake Abuja, yayi masu goma ta arziki.

Baya ga jinjinawa ‘yan wasan bisa gagarumin nasarar da suka samu na lashe gasar kwallon Kwando na mata na nahiyar Afirka, shugaba Buhari, ya kuma bada umarni a baiwa kowanen su Naira miliyan daya (N1Million) kuma Naira dubu dari biyar ( N 500,000) ga jami’an kungiyar na masamman.

Shugaban ya bayyana haka ne gabani fara taro majalisar Ministoci yau a Abuja, inda ya kara da cewa ‘yan wasan sun baiwa marada kunya da wannan nasarar, da kuma cewa Najeriya na alfahari dasu.

Jagoriyar kungiyar Aisha Muhammad, ta ce wannan karamci da aka nuna masu zai kara masu lkarfin gwiwar tunkarar Zinari a gasar wasan Kwando na mata da za a yi a shekara mai zuwa a kasar Spain.