Shahararren kamfanin yanar gizo na Google, na gunar da wani ciniki don sayen kamfanin kera wayoyi na HTC. Kamfanin na google na wani yunkuri na kara fadada karfin kamfanin, wajen samar da yanar gizo mai sauki a duniya.
Kamfanin sun ware tsabar kudi dallar Amurka billiyan $1.1B, don siyan kamfanin. Wannan cinikin ya kara bayyanar da irin shirin kamfanin, na kokarin ganin sun shiga gaban kamfanonin Apple, da Amazon wajen ganin suke kangaba a duniya kimiyya da fasaha.
Tun kimanin shekaru da suka wuce kamfanin na Google, suke kokarin barin kera wayoyi masu manhajar Android, da niyyar samar da wayoyi masu dauke da manhajar iSO, wanda kamfanin kasar Taiwan HTC, suke da karfi wajen amfani da yanar gizo.
A shekarar da ta gabata ne kamfanin na google su kayi wani yunkuri, wanda suka kaddamar da wata wayar hannu, da sifika maras aiki da waya, da take aiki da yanar gizo kai tsaye. Duk dai da cewar, ya zuwa yanzu mafi akasarin wayoyin da ake amfani dasu a fadin duniya, kashi 4 cikin suna amfani da manhajar android ne.
A cikin harajin da kamfanin google ke cigaba da karba daga sauran kamfanoni kamar su Apple, da dai sauran kamfanoni ta irin yadda mutane ke amfani da wayoyin su, wajen samun labarai da bayanai a shafin na google, zai tai makama kamfanin wajen cinma burin su na samar da waya mai kyau da inganci cikin sauki.