Abida Ibrahim Sabo: Matashiya Mai Sana'ar Girke-Girke

Abida Ibrahim Rabo

Wakiliyar Dandalin VOA Baraka Bashir, a wannan karon ta samu hira da Abida Ibrahim Rabo mazauniyar jihar Kaduna wacce take aikin sarrafa abinci da ababan sha ga taruka da wuraren bukukuwa tare da hada bukukuwa.

Ta ce kimanin shekaru 8 kenan da ta fara harkar girki, ko da dai tun kafin wannan lokaci tana da sha'awar girke-girke, inda takan kirkira girki da kanta ko ta kalla a talabijin.

Abida ta ce ba zata iya fadin ko da Naira nawa ta fara sana’arta ba, amma a cewar ta tana da kayan aikin da take amfani da su a gida wanda da su ta fara, sai Naira 40, 000 da ta saka domin sayo wasu kayayyakin fara sana’arta ta girke-girke.

A yanzu dai ta ce tana kimanin miliyan 12 na kayyakin da take girke-girke, bayan kayan abinci da ta ke da su a ajiye.

Ta kara cewa tana kimanin mutane goma sha biyu da suke aiki a karkashinta, bayan wadan da suke zuwa su koyi aiki a wajenta duk da ba ma’aikatanta ba ne.

Daga cikin kalubalen da take fuskanta shine yadda al’umma ke kallo yadda take cudanya da mutane mussamam wadanda suke zuwa domin yin aiki da ita, wanda yakan zamo kalubale ga ita.

Ta ce wajen neman tallafin kudi domin bunkasa sana’a yakan zama wani kalubale babba wanda bayan sun gama bin dukkanin dokoki, sai wata matsala ta shigo ciki wanda ya saba da addini.

Ta ce wannan aiki da takeyi, aiki ne na taimako domin yana bata damar nusar da alumma dangane da irin nau’in abincin da ya dace mutane su ci.

A saurari cikakken rahoto daga wakiliyar Dandalin VOA Baraka Bashir.

Your browser doesn’t support HTML5

Abida Ibrahim Sabo: Mai Sha'awar Girke Takuma Kirkiro Girki Da Kanta