Wai shin wane irin mataki kuke dauka don kare kanku, iyalanku kai harma da al’umah baki daya. A yunkuri da hukumomi keyi don ganin an samar da nagartatun hanyoyin sarrafa abinci da tsaftace muhali da ma Majalisar Dinkin Duniya, sun ware yau a matsayin ranar abinci ta duniya, makasudin wannan shine don kara wayar da kan al’uma dangane da mahimancin cin abinci mai gina jiki da ma tsafta.
A wasu bincike da aka gudanar da ya nuna cewar kimanin mutane miliyan biyu ne ke mutwa a duk shekara, wanda ya hada da ma yara a fadin duniya sanadiyyar rashin abinci me gina jiki da tsafta. Don sanin illolin cin abinci maras gina jiki da tsafta, Dr. Kabir Ibrahim Getso, na asibitin koyarwa ta jami’ar Bayaro da ke kano.
Yayi karin haske a kan hakan, inda yake cewar akwai cituttuka guda biyu da ake kamuwa da su a sanadiyyar rashin cin abinci me tsafta, sun hada da wadanda ake kamuwa da su a cikin sinadaran abincin kana da rashin tsafta, wanda hakan kan haifar da kamuwa da cutar kwalara.
Shima babban sakataren lafiya ta jihar Kano Dr. Dahiru Musa, ya kara kiraga gwamnati dama al’uma su bada hima wajen tsaftace muhalli, ruwan sha dama kanyan gona kamin amfani don samun ingantaciyar rayuwa a kasar baki daya.