Addu'a Da Yin Adalci Sune Zasu Magance Tashin Hankali In Ji Dankwambo; da sauran labaran Najeriya, Afirka da Duniya - 23/03/2014

Gwamnan jihar Gombe Ibrahim Dankwambo

NAJERIYA - GOMBE - Gwamna Ibrahim Hassan Dankwambo, na jihar Gombe, yace manyan abubuwa biyu da zasu kawo karshen tashin hankalin da ake fama da shi a yankin arewa maso gabas sune addu’a da kuma adalci daga bangaren shugabanni. Gwamnan yana magana ne cikin shirin Dandalin VOA, inda yace adalci da addu’a sune suke taimakonsu a Gombe wajen rigakafin tashe tashen hankulan da ake gani a makwabta. Jihar Gombe dai tana makwabtaka da jihohin Yobe da Adamawa, biyu daga cikin jihohin da suke karkashin dokar ta baci, kuma inda ‘yan Boko Haram suke kai hare-hare.

NAJERIYA - ZAMFARA - Gwamna Abdulaziz Yari na Jihar Zamfara yace tashin hankalin da ake fama da shi a wasu sassan Zamfara, batu ne dake neman a zauna da bangarorin. Yace dukkan wadanda ke da hannu a wannan tashin hankalin 'yan Najeriya ne da aka sansu, kuma tilas a tattauna da su kan yadda za a shawo kan matsalolin da suke haddasa su fada da juna. Kwanakin baya ‘yan bindiga suka kashe mutane masu yawan gaske a wasu garuruwa na jihar da makwabciyarta Katsina. Wasu daga cikin tashe tashen hankulan kuma ana danganta su ne da gungun ‘yan fashin da suka addabi mutane, suke kuma kai farmaki a kan kauyuka da garuruwa idan ‘yan banga sun kama ko sun kashe wasu daga cikin ‘yan fashin.

AFIRKA - LIBYA - Wani jirgin ruwan dakon mai dauke da tutar Koriya ta Arewa wanda ‘yan tawayen Libya suka yi ma lodin mai ba tare da iznin hukuma ba, ya koma kasar ta Libya. Yau lahadi jirgin ruwan mai suna Morning Glory yake shiga tashar ruwa ta Zawiya a kusa da Tripoli, inda zai sauke wannan danyen mai. A makon jiya sojojin Amurka suka tare wannan jirgin ruwa a kusa da tsibirin Cyprus, domin hana ‘yan tawayen na Libya kin bin umurnin gwamnati. ‘Yan tawaye sun yi lodin kimanin ganga dubu 234 na danyen mai, na kimanin kudi dala miliyan miliyan 24, a tashar jiragen ruwa ta Sid dake gabashin Libya.

DUNIYA - MALAYSIA - A yau ma dai haka ba ta cimma ruwa ba a neman jirgin saman fasinja na kasar Malaysia da ya bace, duk da sabon rahoton da Faransa ta bayar na hango wani tarkacen da ake zaton ko na garewanin jirgin ne a tekun Indiya. Jiragen sama da na ruwa na kasashe da dama sun yi ta karade wannan yankin teku mai tazarar kilomita dubu 2 da 500 a kudu maso yamma da Australiya a rana ta 4 a jere, amma ba su samu wani abu muhimmi ba. Za a ci gaba da binciken gobe litinin.