Gobe 24 ga watan Maris ce ranar da hukumar kiwon lafiya ta duniya ta ware a matsayin “ranar Cutar Tarin Tibi” cutar da ake kira tarin Fuka. Hukumar kuma na duban wata sabuwar dabara da za a kawas da cutar daga doron duniya. Cibiyar ta kiwon lafiya ta yi kira ga kasashen duniya da su bada goyon baya wajen kawas da dadaddar cutar, nan da shekaru 20 masu zuwa.
An sami gagarumin cigaba wajen yaki da cutar Tibi a cikin ‘yan shekarun da suka gabata. Tsakanin shekarar 2000 da 2013, an iya cetar rayuka miliyan 37 ta hanyar gano cutar da kuma magance ta, amma hukumar ta kiwon lafiya ta ce har yanzu akwai sauran aiki wajen magance cutar.
Daraktan shirin kawasda cutar na hukumar kiwon lafiya Mr. Mario Raviglione, yace shirin kawas da cutar Tibi wata dama ce ta tarihi wadda zata share cutar da tayi sanadiyar lakume rayuka da dama, da kuma kawo rashin lafiya da wahala na tsawon shekaru da yawa.
Cutar Tibi cuta ce da ake iya daukar ta a iska. Kuma ita ce cuta ta biyu da ake dauka, wadda kuma ke kisa bayan cutar kanjamau. Fiye da kashi 95 cikin 100 na mace-macen da aka samu sanadiyar cutar sun faru ne a kasashe masu tasowa.
Muhimmiyar nasarar da ya kamata a cimma nan da shekaru 5 masu zuwa ita ce kawasda bala’in makudan kudaden da masu cutar da iyalansu ke kashewa.
Shirin na hukumar kiwon lafiya zai bukaci gwamnatoci su dauki muhimman hanyoyin da zasu taimaka wa shirin na Tibi, haka kuma shirin ya jaddada bukatar yin amfani da sabbin kayayyakin aiki, da kuma zurfaffa karin bincike akan cutar.