Alakar Mata Masu Shaye-shaye Da Samartaka

Shirin samartaka na wannan makon ya duba yadda kasashen duniya da dama ke fama da matsalar shaye shayen da matasa ke yi musamman mata, wandanda ake alakantasu da matsalolin rabuwar aure, rashin aikin yi ga mazajensu, yaudara daga sauran abokan zama da sauran wasu hanyoyi makamantan su.

bincke ya nuna yadda matasa mata ke dilmiya cikin irin wannan yanayi na shaye shaye ta hanyoyi da dama ba tare da iyayensu ko mazajensu sun sani ba musamman a kasashe masu tasowa.

kamar yadda muka ji daga bakin matasa maza wadanda suka dade suna wannan mummunar harka, kuma kasancewar su matasa masu 'yan mata, da dama, sun dilmiyar da abokan soyayyarsu cikin irin wannan harka ba tare da sun sani ba.

Ku Duba Wannan Ma Aure Baya Hana Neman Ilimi - Dr Maryam Sani Ado

A cewar su, bayan soyayya ta bunkasa, da wuya masoyi ko masoyiya ta jajirce wajan kin amincewa da tayin da aboki ko kawar soyayya suka yi musamman ma kasancewarsu masu abin hannu.

Amma wani sauri ba gudu ba, shin irin wannan soyayyar na kai labari kuwa?

Ku cigaba da kasancewa tare da mu a shafukanmu na dandalinvoa.com, da voahausa.co. da facebook@voahausa domin tafka maharawa.