Albarka Sana'a Tayi Rana, Tunda Bani A Layin 'Yan Bani-Bani

Da ribar sana’ar sayar da Turare ne har ta kai ni ga saro atamfofi da shadda, wasu lokuttan ma har na saro mayafai domin na sayar.

Aisha Lawal Ayagi, mai sana’ar sayar da atamfofi da shadda da mayafai, wacce ta shafe shekaru biyar tana wannan sana’ar, tana sana’ar hannu ne domin ta zamo mai dogaro da kai.

Duk da cewar ta na aikin ofis, hakan bai sa ta tsaya waje guda domin a halin da ake ciki, idan mace tana neman rufin asirin kanta dole ta kama sana’ar hannu. Ta ce da zarar mutum ya fara sana’a kuma ya jure da yin hakuri sai ka ga Allah ya sanyawa sana’ar albarka.

Albarkar sana’ar dai tayi rana tunda a yanzu sana’ar ta habbaka kuma har tana taimakawa 'yan uwanta da kashe wa kanta wasu bukatun.

Aisha ta ce kamar kowanne mai sana’a babban abinda ya ke ci wa sana’ar hannu tuwo a kwarya shine, yawan karbar bashi da wasu lokutan sukan tauye sana’a ko su ma karya sana’ar baki daya.

Daga karshe ta ce tana mai jan hankalin matasa da su kama sana'ar hannu komai kankantarsa domin huce wa kai takaicin bani bani.

Your browser doesn’t support HTML5

Albarkar Sana'a Tayi Rana, Tunda Bani A Layin 'Yan Bani-Bani 5'10"