Alfanun Sana'a Ba shi Misaltuwa

Mercy Peters

Mercy Peters, wata matashiya mai sana’ar sayar da kayan kwaliya na mata da sutara ta mata da yara ta ce ta fara sana’a ne domin ta dauke wa iyayenta nauyin dawainiya ta yau da kullum domin ta zamo mai dogaro da kai.

Mercy, ta ce tana da shago da take sayar da kayanta bayan da ta lura da cewar sayar da kaya a gida na tattare da kalubale da dama wanda idan ba’a yi sa’a ba har ta kai ga an karya jarin mai sana’a.

Ta ce lokacin da take sayar da kaya a gida mafi yawan lokuta idan aka dauki kayan mai sana’a sai an ja mata rai – a cewarta akwai lokacin da wata mata ta dauki kayanta tare da yi mata alkawarin zata biya bayan kwana biyu wanda ya kai su da mako biyu a karshe kuma ta dawo mata da kayan ba tare ta biya ta ba

Mercy, dai ta bukaci mata su jajirce su kama sana’oin dogaro da kai maimakon zama a gida suna jiran mazajensu ko iyayensu su magance musu kananan bukatu.

Ta kara da cewa babban burinta dai ta zama tana saro kaya tana kuma rarrabawa tsakanin mata yan kasuwa.

Your browser doesn’t support HTML5

Alfanun Sana'a Bashi Misaltuwa