Amfani da Tsuntsaye Wajen Safarar Muyagun Kwayoyi

An kama wata Tantabara, da ake amfani da ita wajen safarar muyagun kwayoyi da suka hada da hodar Ibilis da Tabar wiwi.

Ita dai wannan Tantabara ana daura mata wadannan kwayoyi ne domin kaiwa cikin wani gidan Yari a garin Bucaramanga, ta kasar Colombia.

Jami’an ‘yan Sandan da suka kama wannan Tsuntsuwa, sun ce an samu kama ta ne saboda nauyin kwayoyin da aka daura ma ta har yayi mata nauyi ya kuma hanata tashi sama domin sauka cikin gidan Yari yayi mata wuya.

Hukumomin ‘yan Sanda sun ce an kama Tantabarar ne daf da katangar gidan Yarin inda take kokarin tashi domin sauka a cikin gidan Yarin dauke da kwayoyi masu nauyi gram 45.

Wannan ba shine karo na farko da masu sana’ar fatauci muyagun kwayoyi ke amfani da Tsuntsu wajen safarar kwayoyi ba. A bara ma ‘yan Sanda sun kama wani Akun Kuturu, da aka yi amfani dashi a matsayin dan leken asiri.