An ba Wata Lambar Yabo, har da Kudi Dala 170,000

Shafin Bella Naija na yanar gizo ya fadi cewa Wata ‘yar Najeriya mai suna Mrs. Esther Ibanga, ta sami lambar yabon zaman lafiya ta Japan, mai tafe da ladan kudi har dalar Amurka 170,000.

Mujallar business times ta bada rahoton cewa Mrs. Ibanga dai ta sami lambar yabon ne jiya Talata, saboda gwagwarmayar da ta yi akan yawan hare-hare da sace-sace da ‘yan kungiyar boko haram ke yi a Najeriya.

Mrs. Ibanga kuma ita ce ta kirkiro kungiya mai zaman kanta ta mata marasa bango da ake kira Women Without Walls Initiative a takaice, kungiyar da ke yin gwagwarmaya akan hakkokin mata da yara.