An Baiwa Matan Borno Kayan Tallafi - 12/4/14

NIGERIA - Mata ‘yan asalin jihar Borno, dake zaune a birnin Abuja a Najeriya, sun baiwa ‘yan uwansu mata na jihar Borno wadanda rigingimu suka shafa tallafin abinci da kayan sakawa. Hajiya Ya Bawa Kolo, babbar darekta ce a ma’aikatar mata ta jihar Borno “’yan uwa, wadanda suke aiki a Abuja, mata suka hada kansu, da suka hada kansu, suka hada gudunmuwannan suka aiko mana, buhun shinkafa dubu dari uku da hamsin, da kuma zannuwa da kayan shan shayi.”

NIGERIA - A jihar Neja, sama da mako guda kennan da rasuwar sarkin Agaye, a jihar Neja, marigayi Alhaji Muhammadu Kudu Abubakar, amma har yanzu al-ummar masarautar basu samu sabon sarki ba a masarautar.

NIGERIA - Gwamnan jihar Kaduna, Alhaji Muktar Ramalan Yero yace ba tarin tulin jami’an tsaro ne ke kawo zaman lafiya tsakanin al umma ba. Gwamnan yace “na farko da addu’a, na biyu kuma, dole sai mun girmama junanmu”.

Your browser doesn’t support HTML5

Labaran Najeriya - Asabar - 4'00"