Jami'an hukumar safara da fataucin miyagun kwayoyi sun cafke wasu mutane ta bayanan sirri da muka samu. A cewar shugaban hukumar "munji cewa wasi masu aikata ayyukan assha na cikin Otel mai suna Oriental Hotel dake unguwar Victoria Island, aka ce muna ana tuhumar wasu na nan suna hadiyar muggan kwayoyi.
Muna isa sai muka zarce sai dakin da aka bamu lambar sa, da farko manajan hotel din yana neman ya kawo muna cikas, da muka ga haka sai muka fara kama shi domin, Kenan yana da masaniyar cewa ana aikata danyen aiki a cikin wannan dakin.
Muna kuma shiga muka taras dasu suna kan hadiyar wadannan kudaden da aka dunkule su kamar yadda suka saba nade kwaya. Har lokacin da muka kama su, muka kai ofis bamu san cewa kudine suka nannade suke hadiyewa ba sai da muka kawo na'urar mu ta tantance kwayoyi kuma taki nuna kwaya, Muna bude kulli guda sai muka ga ashe dalar Amurka ce aka nannade kuma ake hadiyewa.
Mutanen sun nannade kullin kamar yadda suka saba nade kwaya kuma da gani kai kasan cewa wanda ya nade wadannan kudin ya kware wajen nade kwaya.
Amma wannan shine karo na farko da muka samu mutum ya nannade kudi ya hadiya. mun sha kama masu hadiye kwaya amma kudi wannan shine karo na farko.
Abinda muka taras an hadiye lokacin da muka samu su shine dala dubu dari da goma sha daya amma adadin kudin dala dari dubu dari da hamsin da shidda ne.
Kuma a anzu muna da mutane 6 yanzu haka a hannu, mutumin da ya kawo kudin, da kanin sa, mutane biyu da zasu hadiye kudin zuwa kasar Brazil, su yan Najeriya ne dake da zama a kasar ta Brazil, sai shahararre wajen nade kudin sai kuma manajan hotel din".