An Dakatar da Farfesan Jami'a Kan Zargin Lalata da Dalibarsa

Jami'a

An dakatar da Shugaban sashen koyarda aikin Lauya na Jami’ar Calabar Farfesa, Cyril Ndifon, daga aiki biyo bayan zargin sa da aka yi na tilasta yin lalata da wata dalibar Jami’ar.

Kwamitin da shugaban Jami’ar, Farfesa, Ivara Esu, ya kafa domin bin Kadin zargin ne ya zartar da wannan dakatarwan.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Farfesa Ndifon, da ake zargi da aikata wanna ta’asa shine Farfesan Sharia na farko a jahar ta Cross River.

Shi dai wannan Farfesa, da ake zargi jami’an ‘yan Sanda a jahar sun tsare shi wanda daga bisani aka sake shi kafi ita kuma hukumar Jami’ar, ta dakatar da shi.

Kakakin rundunar ‘yan Sandan Jahar, Mr. Hogan Bassey, yace rundunar na ci gaba da bincike , ya kara da cewa batun fyade ko tursasa yin lalata abu ne dake bukatar natsuwa.