WASHINGTON, DC —
Kimanin tsagerun Niger Delta, hamsin ne da suke mallaki matatun mai, ba bisa ka’ida ba ne, jami’an tsaro na farin kaya na Najeriya, watau NSCDC, suka damke, a jihar Rivers.
Hukumar tsaron ta ce kimanin matatun mai goma sha biyar ne aka lalata a wurare daban daban a yakin Niger Delta.
Kwamadan hukumar tsaron Abdullahi Muhammad, a wata ganawarsa da manema labarai, a Abuja, ya ce wadanda ake zargin an damke su ne ranar laraba, da dare, a wani aiki na masamman da jami’an hukumar suka gudanar a jihar Rivers.
Ya kara da cewa ana tantance wadanda aka damken domin tabbatar da masu hannu a fashe fashe bututun mai a yankin na Niger Delta. Duk wanda aka samu da hannu in ji kwamandan za’a tuhumeshi da laifin yiwa kasa zagon kasa.