An Ga Dalibai Mata Da Aka Sace Daga Chibok An Wuce Da Su Ta Hanyar Monguno - 24/4/2014

Dan majalisar wakilan tarayya mai wakiltar mazabar da ta hada da Monguno a Jihar Borno, Mohammed Tahir Monguno, yace rahotanni daga mazabarsa sun fada masa cewar an ga yaran nan mata dalibai da aka sato daga wata makaranta a Chibok an shige da su ta cikin yankin Monguno, kwana guda a bayan da aka sace su.

Haka kuma, yace a kan hanyarsu ta wucewar, an tsaya a wani gari mai tazarar kilomita 30 daga Maiduguri, inda aka aurar da wasu daga cikinsu ga 'yan bindigar da suka sato su, kuma a bainar jama'a, inda mutane da yawa sun shaida, kuma jami'an tsaro kansu sun san wannan.

Dan majalisar yace daga inda aka sato su a Chibok zuwa inda aka gansu a wani gari mai suna Shuwaram, tafiyar kusan kilomita 200 ne. Yana mamakin yadda za a yi har a yi wannan doguwar tafiya da su ba tare da jami'an tsaro sun tare su ba a cikin jihar da ake dokar-ta-baci.

Your browser doesn’t support HTML5

An Ga Dalibai Mata Da Aka Sace An Wuce Da Su A Yankin Monguno In Ji Dan Majalisa - 2'04"