An Kashe Daruruwan Mutane A Gamboru-Ngala - 7/5/2014

Boko Haram

Ana fargabar cewa an kashe daruruwan mutane a wani harin da 'yan bindiga suka kai kan wani garin dake kan iyakar Najeriya da Kamaru a Jihar Borno.

jami'an jihar sun ce mayakan Boko Haram sun far ma garin Gamboru-Ngala a cikin daren litinin, suka cinna wuta a kantuna da gidaje tare da harbin mutanen garin da suke ayi kokarin gudu.

Kamfanin dillancin labaran AP ya ambaci kwamishinan yada labarai na Jihar Borno, Mohammed Bulama, yana fadin cewa an kashe mutane da dama a harin. Yace ba ya da karin haske kan wannan lamari saboda garin na cikin lungu.

Boko Haram ta sha kai irin wadannan hare-hare kan garuruwa a yankin a can baya.