An Sanya Fam Miliyan 196, Akan Neymar

A cigaba da wasannin share fage da akeyi na International Champion Cup, A jiya kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta doke takwararta ta Real Madrid da ci 2-1 a bugun daga kai sai mai tsaron gida, bayan da aka tashi wasan 1-1.

A yanzu haka Manchester United ita ke mataki na daya a rukunin da maki 5, Tottenham tana mataki na biyu da maki 3, Barcelona maki – 3, PSG maki – 2, Real Madrid maki- 1, Roma maki- 1, Juventus maki- 0, Man City maki- 0.

A hada hadar yan wasan kwallon kafa na duniya kuwa, Benjamin Mendy dan shekara 23, da haihuwa ya zama dan wasan baya mafi tsada a fagen tamola bayan da ya Koma kungiyar Manchester City daga Monaco akan zunzurutun kudi fam miliyan £52.

Roma tace har yanzu bata fidda rai ba wajan ganin ta sayo dan wasan gaba na Leicester City mai suna Riyad Mahrez inda tace dan wasan shine ke kan gaba cikin jerin ‘yan wasan da take da bukatar kawoshi kulob dinta a kakan wasan bana.

Arsenal tana zawarcin dan wasan Sporting Lisbon mai suna William Carvalho dan shekaru 25 a duniya, inda Manchester United da Arsenal suka shiga sahu daya wajan neman sayen dan wasan gefe na Real Madrid Marco Asensio.

Kungiyar PSG ta matsa kaimi don ganin ta kawo Neymar daga kungiyar Barcelona inda ta sakama masa zunzurutun kudi far fam miliyan £196.

Your browser doesn’t support HTML5

An Sanya Fam Miliyan 196, Akan Neymar - 4'55"