An Sayar Da iphone 6s da 6s Plus Miliyan 13 Cikin Kwanaki Uku

APTOPIX Apple

A jiya Litinin ne kamfanin Apple yace ya sayar da sabuwar wayarsa ta iphone 6s da 6s Plus har miliyan 13, daga ranar Juma’a zuwa ranar Lahadi, wato kwanaki uku kenan da fitar da wayar kasuwa.

Wannan ciniki da kamfanin ya samu ya zamanto wani abin tarihi ga kamfanin, a bara ne Apple ya sayar da wayar iphone har miliyan 10 wato shekara guda kenan.

A karshen makon nan da ya wuce ne dai kamfanin yaga cinikin da bai taba gani ba, duk da yake sauran kamfanoni na fitar da sabbin wayoyi masu saukin kudi, adalili haka ne kasuwar Apple ke durkushewa.

Shugaban kamfanin Apple Tim Cook, yace “cinikin da akayi na wayoyin iphone 6s da iphone 6s Plus ba karamin abu bane, ya kuma take tarihin da muke da shi a baya na yawan wayoyin da muka sayar a farkon kwanaki uku da fara sayarwa.”

Cinikin da aka gani bayan kaddamar da sabbin wayoyin na Apple, yazo ne a bisa yadda kamfanin ya tsara wayoyin sa, amma cinikin mako guda ba yana nunin cewa wayoyin zasu dade suna cin kasuwa bane. A shekarar da ta wuce lokacin da Apple ya fitar da wayoyinsa biyu iphone 6 da iphone 6 Plus, wadanda suka zo cikin fasali irin na manyan wayoyi kuma suka karbu da zamantowa wayar da kamfanin yafi sayarwa a tarihi.