An Umarci Matasa Dasu Kaucewa Bautar 'Yan Siyasa

Dr. Usman Bugaje

An umarci matasan Najeriya, dasu hada kai domin kaucewa bautar ‘yan siyasar kasar.

Dr.Usman Bugaje, shugaban kungiyar nazari da Ci gaban arewa kungiya mai zaman kanta ne ya furta haka a wani hira da muryar Amurka.

Ya ce yakamata matasan Najeriya, su yiwa kansu matashiya na sanin inda suka dosa da kuma abunda suke so, da abunda ya kamata su yiwa kansu.

Ya kara da cewa babu wanda zai saurare matasa sai har matasa suna da wani abunda idan ba a saurare ku ba zaku iya hanawa.

Yana mai cewa “Amma idan baku iya hanawa baku iya sawa, toh dan siyasa dai irin na Najeriya, nay au babu tabas cewa zai kula da ku bale ya saurareku.”

Dr. Bugaje ya ce zai zama da alfanu idan har matasan Najeriya, suka yi taro domin nemawa kasu qibla daya domin ci gabansu da kasa baki daya.