Shahararen dan wasannan me suna Salman Khan, na kasar Indiya, ya fuskanci shari’a inda aka yanke mishi daurin shekaru fiyar a gidan kasu. Dalilin wannan hukunci shine, a shakarar 2002 an sami Salman Khan da laifin buge wani mutun da kuma hakan yayi sanadiyar mutuwarshi, wani mazauni kasar Indiyar Isyaku Yaro, da yake karatu a kasar yayi karin haske dangane da yadda abun yake.
A wannan shekarar ta 2002 shi dai shahararen dan wasannan Salman khan suna tafiye a cikin motarshi tare da direba, sai direban ya buge wani mutum, wanda akasame shi direban da laifin yasha barasa, a wannan dalilinne kotu ta yanke ma Salman Khan hukuncin gidan kasu na tsawon shekaru fiyar.
Wannan na nuni da cewar babu wanda yafi karfin doka ko ace yafi wata hallitta, a kasar ta Indiya. Duk wanda yayi ba dai dai ba, to za’a hukumtar da shi dai dai da abun da ya aikatar.