A jiya Alhamis 28 ga watan tara 2017 kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich, dake kasar Jamus ta bada sanarwar sallamar mai horar da ‘yan wasan kiungiyar Carlo Ancelotti, daga kungiyar.
Kungiyar ta bada wannan sanarwar ne jim kadan bayan kwana daya da kungiyar ta sha kashi da ci 3-0 a hannun Paris Saint-Germain, na kasarsa faransa, a wasan gasar cin kofin zakarun nahiyar turai (UCL) na shekara 2017/18 a matakin wasan rukuni a ranar laraba.
Kungiyar tace Ancelotti yana da laifi wajan rashin samun nasara a wasan.wanda sakamakon haka yasa kungiyar take mataki na biyu a rukunin (B) da maki ukku, a wasannin biyu da ta buga.
Haka ma a wasanta na gida wato Bundesliga 2017/18 na kasar Jamus, nan tana mataki na biyu daga saman teburin da maki 13, a wasannin mako na shida.
Carlo Ancelotti mai shekaru 58, da haihuwa dan kasar Itali ne ya dawo kungiyar Bayern Munich, a shekara 2016, daga kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, na kasar Spain, a 2015.
Ya jagoranci kungiyoyin kwallon kafa da dama a kasashe daban daban tun daga shekara ta 1995 a kungiyar Reggiana na kasarsa ta haihuwa Itali, zuwa 1996,
Da kuma kungiyar Parma, 1996 – 1998, Juventus, 1999 – 2001, Milan, 2001 – 2009 da Chelsea, 2009 – 2011.
Sai kungiya kwallon kafa ta Paris Saint Germain, a shekara ta 2011 – 2013, daga nan ya Koma Real Madrid, 2013 – 2015, inda a shekara ta 2016, ya Koma Bayern Munich.
Your browser doesn’t support HTML5