Shugabanin majalisar dokoki, da masu sa ido a Amurka da Turai, da kuma jami'an ma'aikatar harkokin wajen Amurka sun fara hurawa kamfanin Facebook wuta akan wasu sabbin zarge zarge gameda yadda aka yi amfani da babban kamfanin sada zumuncin a lokacin zaben shugaban kasa na shekarar 2016 a Amurka.
Wani Kwamitin kasuwanci a majalisar dattawa ya tura tambayoyi ga kamfanin akan zargin cewa kamfanin sarrafa bayanai, da ake kira Cambridge Analytica yayi amfani da bayanan masu amfani da Facebook miliyan 50 don taimakwa a yakin neman zabe. Yan majalisar Amurka da Burtaniyya sun Kira shugaban kamfanin na Facebook Mark Zuckerberg don ya bada bahasi. Kamfanin ya gana da ma'aikatansa jiya talata don tattauna yadda Zasu tunkari tambayoyin da Za a yi masu
Daya da cikin manyan tamabayoyin da aka yi masu ita ce, "me ya sa kamfanin bai sanar da wadanda abin ya shafa ba gameda batun? Ranar litinin, hannun jarin kamfanin ya fadi da kusan kashi 7, in da yayi hasarar kimanin dala miliyan 36.