Arsenal Ta Kauracewa Kalaman da Ozil Ya Yi Game Da Al'ummar Kasar Sin

Tsohon mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal Arsene Wenger ya bayyana cewar dan wasan Arsenal Mesut Ozil, ya na da damar fadin albarkacin bakinsa.

Wenger ya ce maganar da Ozil ya yi akan al'ummar kasar Sin, ya yi ne a kashin kansa ba da sunan Arsenal ba.

A kwanannan ana samu takun saka tsakanin al'ummar kasar Sin da Mesut Ozil dan gane da maganar da dan wasan ya yi na cewar ana muzguna wa musulmai kabilar Uighur dake yankin Xinjiang.

Hakan bai yi wa al'ummar kasar Sin dadi ba, inda duk wasu magoya bayan Arsenal a kasar suka kaurace wa duk wani an da ya shafe kungiyar har ma suka kona riguna masu alamar kulob din.

Bayan haka, sun bukaci a Arsenal ta sallami Ozil daga kulob din ko kuma suma su kaurace wa duk wani abin da ya shafeta, hakan ma ya sa gidan talabijin ba CCTV ya kaurace nuna duk wasannin da Arsenal ta keyi.

Sai dai ita ma a nata bangaren, Arsenal ta kauracewa maganganun Ozil, a kungiyance ta ce kowa na tane.

Arsene Wenger ya ce sam bai kamata wannan batu ya shafi kungiyar sa ta Arsenal ba, domin ba da yawunta yayi maganar ba.