Rundunar ‘yan Sandan jahar Lagos ta cafke wani matashi mai suna Ayodele Adedeji, da yayi Sojan goma a unguwar Onipanu, wanda ke ikirarin cewa shi Soja ne.
Adedeji dai dubun shi ya cika ne a lokacin da wasu matasa basu amince da take taken shi ba sai suka gyayyato wani dan Sanda wanda ya tuhume shi daga bisani aka gano cewa sojan boge ne.
Da aka tuhume shi Adedeji ya amsa cewar ya dade yana yiwa jama’a karyar cewa shi Soja ne.
An samu kayayyakin Sojoji da suka hada riguna da wanduna da katin shaida wato ” I D Card” na jabu da Takalmi da kuma bindigar boge da wasu abubuwa.
Kwamishinan ‘yan Sandan jahar ta Lagos, Abdulmajid Ali, ya umarci mataimakin kwamishinan ‘yan Sanda mai kula da bangaren bayanan asiri da yayi bincike ko yana da hannu a sace sacen mutane da ake yi ko kuma fashi da makami.